ABNA24 : Shafin yanar gizo na labarai ‘africanews’ ya nakalto shugaban yana fadar haka a jiya bayan haduwarsa da daya daga cikin shuwagabannin kasashen Sahel a birnin Paris babban birnin kasar ta Faransa.
Labarin ya kara da cewa sojojin da za’a ragen dai sun hada da wadanda suke aiki tabbatar da tsaro a arewacin kasar Mali, wadanda suka hada da na sansanonin sojojin Faransa a Timboktu, Kidal da kuma Tessalit. Sai dai shugaba ya ce zai rahe sojojin 2500 -3000 daga sojoji 5100 da suke arewacin kasar ta Mali.
Sojojin da zasu wanzu a kasar zasu ci gaba da taimakawa kasashen a yakin da suke fafatawa da yan ta’adda a yankin.
Daga karshe shugaba Macron ya ce kasar Faransa za ta ci gaba da zama kawar kungiyar G5 Sahel wadanda suka hada da Niger, Mali, Borkina Faso, Chadi da kuma Mauritania.
342/